An kashe wasu ‘yan bindiga uku tare da kwato makamai da alburusai

0 138

Dakarun runduna ta 6 ta sojojin Najeriya dake Jalingo babban birnin jihar Taraba sun kashe wasu ‘yan bindiga uku tare da kwato makamai da alburusai.

An kai samame na musamman a kauyen Chibi dake karamar hukumar Karim-Lamido ta jihar, bayan samun rahoton sirri.

Matakin da sojojin suka dauka cikin gaggawa, a cewar Kwamandan rundunar, Birgediya Janar Kingsley Uwa, ya kai ga kawar da masu laifin tare da kwato wasu muhimman abubuwa.

Daga cikin kayayyakin da aka kama akwai bindigogi kirar AK-47 guda biyu, babura da ’yan ta’addan ke amfani da su, da wani akwati mai dauke da harsashi guda 40. Da yake yaba wa sojojin bisa jajircewarsu da kuma yadda suke gudanar da ayukkan su, ya jaddada kudirin sojojin na kawar da masu aikata laifuka a Taraba tare da baiwa mazauna jihar tabbacin ci gaba da kokarin wanzar da zaman lafiya da tsaro.

Leave a Reply

%d bloggers like this: