Majalisar dokokin jihar Jigawa ta duba ayyukan da karamar hukumar Birniwa

0 152

Tawagar kwamatin lura da kananan hukumomi na majalisar dokokin jihar Jigawa ta duba ayyukan da karamar hukumar Birniwa ta gudanar a karkashin Asusun Magance Matsalolin Muhalli na Kasa na shekarar 2023.

Daya daga cikin yan kwamatin da ya jagoranci tawagar, Alhaji Lawan Muhammad Dansure, ya ce ziyarar a karo na biyu ta biyo bayan korafi da wasu kamsiloli suka yi na rashin masaniya game da ayyukan a lokacin rangadin kwamatin a watan December 2023.

Ya ce tawagar ta duba aikin ginin fadar Hakimin Kazura wadda karamar hukumar ta Birniwa da kan ta ta kirkiro da aikin kuma an kammala shi yayin da aka gina kwalbati a Kazura a karkaahin Asusun Magance Matsalolin Muhalli na Kasa.

Alhaji Lawan Muhammad Dansure ya bayyana cewa sun duba aikin kwalbati da cikon kasa da aka yi a kauyen Isfari yayin da aka gina magudanin ruwa a kashi na biyu na aikin dan magance ambaliyar ruwa.

Haka kuma tawagar kwamatin ta duba aikin magudanin ruwa wadda aka rufe da slab a Birniwa Kofar Fada da kuma wani magudanin ruwan da cikon kasa a Unguwar Mangawa.

Alhaji Lawan Dansure ya ce a yanzu dai tawagar ta gamsu cewa an gudanar da wadannan ayyuka da kamsilolin ba su da masaniya akai illa gibi da aka samu wajen sadarwa tsakaninsu da majalisar karamar hukumar.

A jawabinsa mukaddashin shugaban karamar hukumar Birniwa Bello Wakili ya yaba da wannan ziyara  tare da bada tabbacin yin amfani da gyararrakin da kwamitin ya bayar Yace karamar hukumar tana aiki tare da majalissar kamsiloli da maaikata domin ciyar da yankin gaba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: