An kwashe maniyyata sama da 16,000 a cikin kwanaki goma na farko – NAHCON

0 107

Hukumar alhazai ta Najeriya ta kwashe maniyyata sama da 16,000 a cikin kwanaki goma na farko tun bayan da hukumar ta fara jigilar maniyyata zuwa kasa mai tsarki domin gudanar da aikin hajjin shekarar nan.

A ranar Alhamis 16 ga watan Mayun 2024 ne jirgin farko na maniyyata na bana na shekarar 2024 ya isa Madina a kasar Saudiyya, bayan ya tashi daga filin jirgin saman Sir Ahmadu Bello da ke Birnin-kebbi, babban birnin jihar.

A cikin jirgin na Flynas wanda ya taso daga Kebbi zuwa Madina da karfe 4:54 na yammacin ranar Laraba,a ranar 15 ga watan Mayu yana dauke ne da mutane 422 wadanda suka hada da maza 269, mata 153, da jami’an jirgin bakwai. Tuni dai hukumar ta kammala tashin jirage 40 cikin nasara, inda adadin maniyyata 16,794 da suka hada da maza 9,794 da mata 7,003 aka dauke su zuwa kasa mai tsarki a garuruwan Madina da Jeddah.

Leave a Reply

%d bloggers like this: