An kama wani dan Bindiga mai suna Muhammad Bello, wanda ke da alaka da Dogo Haliru

0 213

Rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna ta ce jami’anta sun kama wani dan Bindiga mai suna Muhammad Bello, wanda ke da alaka da Dogo Haliru.

Hakan ya biyo bayan ceto wasu mutane uku da aka yi garkuwa da su a hanyar Kindandan zuwa Dogon Dawa a karamar hukumar Birnin Gwari.

A wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna, ASP Mansir Hassan, ya fitar, ya bayyana cewa kwamishinan ‘yan sandan jihar ya yabawa jami’an da suka yi wannan  aiki, kamar yadda ya ba da umarnin kara karfafa sintiri a yankin. A ranar 21 ga watan Mayu, Rundunar reshen Kidandan ta samu kiran waya da bayyana cewa wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun tare hanyar Kidandan zuwa Dogon Dawa tare da yin garkuwa da wasu mutane da ba a tantance adadinsu ba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: