An rufe tare da rusa babbar kasuwar Madalla dake Suleja

0 170

Hukumomi a jihar Neja sun rufe tare da rusa babbar kasuwar Madalla ta mako-mako a karamar hukumar Suleja.

Kasuwar wadda take haifar da cinkoso mai tarin yawa a kan babbar hanyar Abuja zuwa Kaduna, ta dade tana ciwa matafiya tuwo a kwarya da kuma jami’an yankin baki daya.

Gwamna Mohammed Umaru Bago, a lokacin hawan sa kan karagar mulki, ya yi alkawarin sauya wa kasuwar matsugunni a wani bangare na shirin gwamnatinsa na sabunta birane. Hukumomin Karamar hukumar Suleja da ke kula da kasuwar ne suka rusa ginin kasuwar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: