Najeriya na aiki tukuru domin kawar da ayyukan ta’addanci – Bola Tinubu

0 151

A jiya Juma’a ne shugaban kasa Bola Tinubu ya karbi bakuncin daraktan hukumar binciken manyan laifuka ta kasar Amurka (FBI), Christopher Asher Wray, inda ya tabbatar masa da cewa Najeriya na aiki tukuru domin kawar da ayyukan ta’addanci, da aikata laifuka ta yanar gizo da sauran miyagun laifuka.

Shugaba Tinubu ya bayyana haka ne a wata ganawa da ya yi da Christopher Asher Wray a fadar gwamnati da ke Abuja, inda ya yi kira da a hada kai tsakanin Najeriya da sauran kasashen yammacin Afirka domin kawar da miyagun laifuka.

Shugaban kasar ya ce gwamnatinsa ta baiwa ilimi fifiko a matsayin wani makami na yaki da fatara da ake kyautata zaton shi ne ke haddasa miyagun ayyuka.

Shugaba Tinubu ya yi kira ga Amurka da ta tallafa wa kasashe masu tasowa da fasahar kere-kere da musayar ilmi da ake bukata domin yakar manyan laifuka na kasa da kasa.

A cikin jawabinsa, Darakta Wray ya ce ya zo Nigeria ne domin inganta kawancen da ke tsakanin gwamnatin Najeriya da gwamnatin Amurka.

Leave a Reply

%d bloggers like this: