Wani direba ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 6 tare da raunata wasu 7 a jihar Jigawa

0 189

Wani direban mai shekaru 45 mai suna Tasi’u Ashiru ya yi sanadiyyar mutuwar mutane shida tare da raunata wasu bakwai a jihar Jigawa.

Wasu shaidun gani da ido sun shaidawa manema labarai cewa lamarin ya faru ne a ranar Laraba a Sabon Garin Takanebu, cikin karamar hukumar Miga, daura da hanyar Jahun zuwa Gujungu, inda direban ya rasa yadda zai yi da motar ya ci karo da ‘yan kasuwa a kasuwar.

Kakakin rundunar ‘yan sandan, DSP Lawan Shiisu Adam, ya tabbatarwa faruwar lamarin. 

DSP Shiisu ya ce tawagar ‘yan sanda sun garzaya wurin da lamarin ya faru inda suka kai gawarwakin da wadanda suka jikkata zuwa babban asibitin Jahun.

Yayin da ake tsare da direban, kuma ana ci gaba da gudanar da bincike, sannan ya yi kira masu ababen hawa da su yi tuki a hankali tare dayin taka tsantsan, yana mai gargadin cewa duk wanda aka kama yana tukin ganganci ko kuma ya yi sanadiyyar rasa ran mutane ta hanyar tukin ganganci za a kama shi kuma za a hukunta shi a gaban shari’a.

Leave a Reply

%d bloggers like this: