Za’a samar da intanet mai karfi ga manoma a kasashen Kenya da Tanzaniya da kuma Najeriya

0 206

Sanarwar da mataimakiyar shugaban kasar Amurkar Kamala Harris ta yi, ya zo ne shekara guda da ziyarar da kai nahiyar Afirka, a kuma lokacin da suka zanta da shugaban kasar Kenya William Ruto a birnin Washington.

Wannan na daga cikin manufofin Amurkar na karfafa huldar tattalin arziki da nahiyar Afirka, nahiyar da hankali ya karkata kanta a matsayin wacce makomar ci gaba na duniya ya dogara da ita. Bankin bunkasa kasashen Afirka da ma wasu kungiyoyi sun kara himma wajen inganta fannin sadarwar zamani, inda za a fara da samar da Intanet mai karfi ga manoma a kasashen Kenya da Tanzaniya da ma Najeriya a tashin farko kafin abin ya kai ga sauran kasashe na nahiyar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: