An maye sunan sakataran jam’iyyar APC na kasa Abubakar Kyari da Ali Dalori daga jihar Borno

0 230

Kwamitin gudanarwa na jam’iyyar APC ya sanar da sunayen shugabannin kwamitin domin cike gibin wanda babu a cikin kwamitin da shugabannin shiyyoyi.

Sakataran jam’iyyar Ajibola Basiru shine ya sanar da sunayen a yammacin jiya lokacin da yake yiwa manema labarai karin haske dangane da zaman ganawar shugabannin jami’iyyar a helkwatar jami’iyyar ta kasa.

An maye sunan sakataran jam’iyyar na kasa Abubakar Kyari da Ali Dalori daga jihar Borno,yayinda aka mayae sunan shugabar mata Beta Edu da Mary Alile Idele daga Jihar Edo.

Dukkanin mututanen biyun Abukakar Kyari da Beta Edu shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya nada su Ministoci. Beta Edu an nada Ministan bada agaji walwala da yaki da talauci, shi kuwa Kyari ya zama Ministan noma da samar da abinci.

Leave a Reply

%d bloggers like this: