Rundunar sojin saman Najeriya zata samar da jirage masu saukar ungulu guda 18

0 155

Babban hafsan rundunar sojin sama Air Marshal Hassan Abubakar, yace rundunar sojin saman Najeriya zata samar da jirage masu saukar ungulu 18 domin karfafa aikin ta a Najeriya.

Hassan Abubakar, yace jirage masu saukar ungulu kasar Amurka ce zata samar da su, yayinda guda 6 kasar Turkiyya zata baiwa Najeirya a watan satumba.

Ya kuma kara da cewa rundunar sojin saman Najeriya na daukar matan da suka dace domin kawo karshen Hadarin jiragen saman Sojojin sama a Najeriya.

Yace matakan sun hada da binciken sanadin Hadarin jiragen domin kare afkuwar hakan nan gaba.Hassan Abubakar, yace Rundunar sojin saman Najeriya zata cigaba da samar da jirage masu saukar ungulu domin a tabbatar an dena satar danyen mai  matatun mai na Neja Delta.

Leave a Reply

%d bloggers like this: