An raba kudi naira miliyan 134 ga iyalan jami’an ‘yan sanda 25 da suka rasa rayukansu a bakin aiki

0 152

Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta raba kudi naira miliyan 134 ga iyalan jami’ai 25 da suka rasa rayukansu a bakin aiki a jihar Zamfara dake arewa maso yammacin Najeriya.

Sanarwar ta fito ne a cikin wani bayani da kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara, Yezid Abubaker ya raba wa manema labarai a yau Laraba.

A cewar sanarwar, an bayar da kudaden ne ta hanyar inshorar rayuwa, da kuma tsare-tsaren jin dadin iyali na da bababn sufeta janahar na yansandan kasa ya fito dashi.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Zamfara, CP Muhammad Shehu Dalijan, wanda ya wakilci babban sufeton ‘yan sandan Najeriya Kayode Adeolu Egbetokun, ya gabatar da cakin kudi da ya kai miliyan N134, ga iyalan mamatan.

CP Shehu ya jaddada kudirin Sufeto Janar na ‘yan sandan kasar nan na ba da fifiko ga jin dadin ‘yan sandan, walau suna aiki ko kuma bayan mutuwarsu. Ya shawarci wadanda suka ci gajiyar kudaden da su yi amfani da kudaden yadda ya kamata wajen biyan bukatunsu na ilimi da sauran bukatunsu na yau da kullum.

Leave a Reply

%d bloggers like this: