Gwamnan jihar Zamfara ya kafa dokar ta-baci a fannin kiwon lafiyar jihar a hukumance

0 165

Gwamnan ya bayyana hakan ne a yayin wani jawabi da ya ga yan jihar a jiya Talata, inda ya nuna matukar damuwarsa bayan ziyarar da ya kai babban asibitin Gusau.

Gwamnan ya bayyana takaicin sa akan yanayin da ya tsinci asibitin, inda ya bayyana kudurinsa na magance kalubalen da fannin kiwon lafiya na jihar ke fuskanta.

Manyan tsare-tsare da gwamnan ya zayyana sun hada da samarda  ababen more rayuwa da inganta dukkan asibitocin gaba daya ta hanyar samar da kayan aiki na zamani. Gwamnan ya kuma bayyana kudurin sa na samar da walwala ga ma’aikatan kiwon lafiya yayin da ya yi alkawarin samar da tsarin inshorar lafiya mai mai sauki ga daukacin al’ummar jihar Zamfara.

Leave a Reply

%d bloggers like this: