Ziyarar sirri da Bola Tinubu ya yi zuwa Faransa ba zai kawo tsaiko ga ayyukan gwamnati ba

0 123

Bayo Onanuga, mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan yada labarai da dabaru, ya ce shugaba Bola ya na kan sahwo kan kalubalen cikin gida a kasar nan.

Mista Onanuga yana mayar da martani ne kan kalaman da Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP a zaben 2023 ya yi.

Ya ce ziyarar sirri da shugaban kasa ya yi zuwa kasar Faransa ba zai kawo cikas ga ayyukan gwamnati ba, inda ya ce an sanar da ‘yan Najeriya tafiyar.

Ya ce shugaban ya kuma amince da ware Naira biliyan 50 a wani asusu na musamman don magance wasu kalubalen tsaro a yankin Arewa maso Gabas da kuma amince da kudaden da za a yi amfani da su wajen sayen kayan aiki na zamani don gano masu aikata laifuka a babban birnin tarayya Abuja. Mista Onanuga ya yi tir da kalaman Atiku da yake zargin Tinubu da yin katsalandan a cikin wasu matsalolin tsaro da tattalin arzikin kasar nan.

Leave a Reply

%d bloggers like this: