Rundunar tsaro ta Amotekun ta kama wasu mutane 31 da ake zargi da aikata laifuka daban-daba

0 136

Rundunar tsaro ta yammacin Najeriya da akafi sani da Amotekun a jihar Ondo ta ce ta kama wasu mutane 31 da ake zargi da aikata laifuka daban-daban a fadin kananan hukumomi 18 na jihar.

Adetunji Adeleye, Kwamandan rundunar ta Amotekun ne ya bayyana haka yayin da yake gabatar da wadanda ake zargin a gaban manema labarai a ranar Laraba a Akure.

Adeleye ya ce an kama wadanda ake zargin ne da laifukan da suka hada da garkuwa da mutane, mallakar bindigogi ba bisa ka’ida ba da kuma wadanda suka kware wajen fasa shaguna da gidaje.

Kwamandan ya ce rundunar ba za ta yi kasa a gwiwa ba a kokarinta na kawar da masu aikata laifuka a jihar.

Ya kuma ce gwamnati ta jajirce wajen ganin ta tabbatar da cewa masu zuba jari, manoma, mazauna, da matafiya sun yi harkokin su cikin walwala a jihar ba tare da fargabar hare-haren ‘yan bindiga ba. Adeleye ya ce gwamnatin Gwamna Lucky Aiyedatiwa ta umurci shugabannin hukumomin tsaro a jihar da su fatattaki masu aikata laifuka da ke kawo cikas ga zaman lafiya a jihar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: