Shugaba Tinubu ya umarci duka hukumomin gwamnati da su sayi motoci masu amfani da iskar gas

0 96

Shugaban kasa, Bola Tinubu ya umarci duka hukumomin gwamnati da su sayi motoci masu amfani da iskar gas a wani ɓangare na yunƙurin da ƙasar ke yi na komawa amfani da makamashi mara gurɓata muhalli tare da rage tsadar mai.

Umarnin na ƙunshe cikin sanarwar da kakakin shugaban kasar Ajuri Ngelale ya fitar, inda ya ce Tinubu ya ce yana sa ran duka hukumomin gwamnati da ma’aikatu su soma yasar da motocin da suke da su masu amfani man fetur ko dizel.

Shugaban ya ƙara da cewa duka sabbin motocin gwamnati ko babura masu ƙafa uku dole ne su yi amfani da nau’in iskar gas na da hasken rana ko ta hanyoyin makamashi.

Shugaban ya kuma bayyana ƙudirinsa na amfani da iskar gas yadda ya kamata domin magance tsadar sufuri ga al’umma.

Umarnin shugaban ya zo ne ƴan makonni bayan da gwamnati ta sanar da ƙudirinta na samar da motocin bas da babura masu ƙafa uku fiye da 2,000 masu amfani da iskar gas a ƙoƙarin rage tsadar sufuri kafin ranar 29 ga watan Mayun da muke ciki, lokacin da shugaban zai cika shekara guda a karagar mulki.

Leave a Reply

%d bloggers like this: