Buratai ya nuna goyon bayansa ga kin bari sojojin kasashen waje su kafa sansani a Najeriya

0 162

Tsohon hafsan hafsan soji Laftanar Janar Tukur Yusuf Buratai, ya jajirce wajen ganin Nijeriya ta samu ‘yancin cin gashin kai tare da nuna goyon baya ga shawarar Shugaban kasa Ahmed Bola Tinubu ta kin bari sojojin kasashen waje su kafa sansani a qasar nan.

Bayanin Buratai ya biyo bayan zargin da wasu shugabannin Arewa suka yi a baya-bayan nan, na cewa gwamnatocin Amurka da Faransa na neman Nijeriya ta rattaba hannu kan wasu sabbin yarjejeniyoyin tsaro, tare da share hanyar sake tsugunar da sojojin da aka kora daga yankin Sahel.

Ministan yada labarai da wayar da kan jama’a na kasa ya bayyana karara cewa Nijeriya ba ta da wani shiri na tsugunar da sojojin Amurka a kasarmu.

A wata wasika da suka aike wa shugaba Tinubu kwanan nan, wasu daga cikin shugabannin arewa sun yi gargadin cewa kasancewar sansanonin sojan kasashen waje zai kara dagula dangantakar da ke tsakanin Nijeriya da jamhuriyar Nijar da ma makwaftaka da kasar Faransa, inda suka roki shugaban da ya ba da fifiko kan tsaron kasa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: