An sake gabatar da shaidu goma a gaban wata kotun Kano kan zargin kisan yarinya ‘yar shekara 5 mai suna Hanifa Abubakar

0 171

Wani shaidar mai gabatar da kara, Ubale Usman, ya gabatar da shaidu goma a gaban wata babbar kotun Kano a kan zargin kisan yarinya ‘yar shekara 5 mai suna Hanifa Abubakar.

Sawaba ta ruwaito cewa, Abdulmalik Tanko, tare da Hashimu Isyaku da Fatima Musa suna fuskantar tuhume-tuhume biyar da suka hada da hada baki, yunkurin yin garkuwa da mutane da garkuwa da mutane da kuma boye gawa.

Laifukan sun ci karo da wani sassan na dokokin manyan laifuka na Penal Code na jihar Kano.

A dawowar zaman shari’ar a jiya, lauya mai shigar da kara, Babban Lauyan Jihar Kano kuma Kwamishinan Shari’a, Musa Lawan, ya gabatar da shaidu uku a gaban kotun, wanda Ubale Usman na cikin su a matsayin shaida mai gabatar da kara.

Ubale Usman, jami’i ne mai bincike a rundunar yaki da masu garkuwa da mutane ta rundunar ‘yan sandan Kano, ya bayar da wasu kayayyaki da suka hada da wayoyin hannu guda hudu, rigar sanyi da farin hijabi da bajon makaranta da shebur da hoton wacce aka kashe da kuma kudi naira dubu 30 da 300.

Leave a Reply

%d bloggers like this: