Labarai

‘Abubuwan da suka sa na kori ministoci na shida ciki harda ministan kudi’ – Shugaban kasar Mozambique, Filipe Nyusi

Shugaban kasar Mozambique Filipe Nyusi ya kori ministoci shida da suka hada da ministan kudi a wani gagarumin sauyi cikin wata sanarwa da ofishin shugaban kasar ya fitar.

Sanarwar ba ta bayar da wani dalili na korar ministocin ba, bata kuma nuna alamun lokacin da za a nada sabbi ba.

Wannan dai shi ne babban garanbawul na biyu a fasalin majalisar ministocin a watannin baya-bayan nan.

Sauran da aka kora sun hada da ministan albarkatun ma’adinai da makamashi, da ministan kamun kifi, da kuma na ruwa da ayyukan jama’a, da kuma ministan gidaje da albarkatun ruwa.

Masu lura da harkokin siyasa a kasar sun ce ba su yi mamakin korar da aka yiwa ministocin ba.

A watan Nuwamba, shugaba Nyusi ya kori ministocin tsaro da na harkokin cikin gida tare da maye gurbinsu.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: