Karamin Ministan tsaro Bello Matawalle da Gwamnan jihar Yobe Mai Mala Buni, sun tsara yadda jihar zata ci gaba da zama cikin zaman lafiya da kwanciyar hankali tare da fita daga cikin tashe-tashen hankali daga yan tada kayar baya.
Da yake jawabi yayinda ya kai ziyara ofishin karaminin Ministan tsaron,Gwamna Mai Mala yace yana neman hadi dukkan ma’aikatu domin karfafa tsaro a jihar, yana mai cewa an samu cigaba mai yawan gaske ta fuskar tsaro a jihar ta Yobe.
A cewar sa, an samar da dukkan damar-maki da nufin magance duk wata matsala ta tsaro a jihar,inda yace gwamnatin sa na bada goyan baya ga hukumomin tsaro yadda ya kamata domin magance matsalar tsaro.
Da yake jawabi, karamin Ministan tsaron Bello Matawalle ya tabbatar da cewa gwamnatin tarayya zata yi duk abinda ya dace domin kare rayuka da dukiyoyin mutanen Najeriya.