An samu raguwar hadura a watannin farko na wannan shekara da kashi 15.5 cikin 100

0 305

Hukumar kiyaye haddura ta kasa tace an samu raguwar hadura a watannin farko na wannan shekara da kashi 15.5

Mai magana da yawun hukumar na kasa Bisi Kazeem, yace rahotannin da suka tattara ya nuna cewa an samu raguwar haddura da jin raunuka a wannan shekarar idan aka kwanta dana shekarar 2022.

Yace an samu raguwar cunkosun ababen hawa da kashi 14 idan aka misalta dana shekarar 2022,yana mai cewa jami’an hukumar sun samu rahotan haddura kimanin 5,700, a wannan shekarar inda a shekarar gabata a ka samu rahotannin haddura sama da dubu 6,627.

Bisi Kazeem, ya bayyana cewa daga watan Janeru na wannan shekara an samu raguwar samun mutanen da suka ji raunuka da kashi 14, inda aka samu nasarar ceto mutane 16,716 da sukayi hadari, a shekarar data gabata kuwa aka samu mutane 19,440. Yace an samu raguwar mutanen da suka mutu a watanni 6 na wannan shekarar,inda aka samu mutane 2,850 da suka rasu a wannan shekarar, sai kuma mutane 3,375 da suka halaka sanadiyyar haddura a shekarar 2022, wato an samu raguwar mutanen da suka mutu sakamakon hadari da kashi 15.5

Leave a Reply

%d bloggers like this: