Za’a samar da gidan tarihin Mayakan Boko Haram a yankin Arewa maso gabas

0 145

Shugaban hukumar raya yankin arewa maso gabas Mohammed Alkali, yace suna aiki tare da jami’ar Maiduguri da kuma masu ruwa da tsaki domin samar da gidan tarihin Mayakan Boko Haram a yankin.

Mohammed Alkali, ya bayyana haka ne a jiya a Maiduguri yayin tunawa da ranar zaman lafiya ta duniya na wannan shekarar, yace samar da gidan tarihin za’ayi ne da nufin bada labarin mayakan Boko Haram a watan hanya ta daban domin canja tunanin mutane.

Mohammed Alkali, yace gidan tarihin zai baiwa masu ruwa da tsaki damar bada labarin ga yara masu tasowa domin su san illar da yaki yayi a yankin.

Ya kuma kara da cewa hukumar ta shirya domin yaki da ra’ayi mai Tsauri.

Leave a Reply

%d bloggers like this: