A safiyar yau an sace daliban jami’ar tarayya dake Gusau da ba’a kai ga tantance adadin su ba

0 281

An sace dalibai da ba’a kai ga tantance a dadi su ba a safiyar yau, a jami’ar gwamnatin tarayya dake Gasau babban birnin jihar Zamfara.

Yan bindiga masu yawan gaske sun mamaye yankin sabon-Gida dake karamar hukumar Bungudu dake jihar Zamfara.

Wani mazaunin garin Sabon-Gida yace yan bindigar sun mamaye garin ne da misalin karfe uku tare da harbin kai mai uwa da wabi.

A cewar sa, dakuna uku na kwanan daliban aka kaiwa hari inda aka tafi da dalibai masu tarin yawa.

Kauyan Sabon-Gida wanda nan ne babban sashen jami’ar gwamnatin tarayya dake jihar na dana nisan kilomita 20 daga babban birnin jihar Gusau.

Kokarin jin ta bakin hukumomin makarantar dangane da wannan mummunan lamari abun yaci tura.

Kazalika, rundunar yan sandan jihar Zamfara bata tabbatar da faruwar lamarin ba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: