Hukumomin Taliban sun ce akalla mutum 60 ne suka mutu a wata ambaliayr da ruwan sama kamar da bakin kwarya ya haifar a arewacin lardin Baghlan kuma Sama da mutum 100 kuma sun jikkata.
Kakakin ministan cikin gida ya shaida wa manema labarai cewa karin mutane masu yawa sun makale a cikin gidajensu.
Hotunan da aka wallafa a shafukan sada zumunta sun nuna yadda ruwan da ke hankoro ya rika shafe gidaje a kauyuka da dama, ya bar wurare da dama a rushe.
Jami’ai sun ce an yi hasashen samun tsawa a cikin kwanaki masu zuwa wanda hakan zai iya kara adadin mutanen da abin ya shafa.
A yammacin Afghanistan a watan jiya, gwamman mutane ne suka rasa rayukansu a wata ambaliya da aka samu.