An raba kayayyakin agajin gaggawa ga mutanan da suka gamu da iftila’in gobara a karamar hukumar Jahun
Karamar Hukumar Jahun ta raba kayayyakin agajin gaggawa ga mutanan da suka gamu da iftila’in gobara a garin Yalwa da Giwaran.
Mataimakin shugaban Karamar Hukumar Alhaji Sani Hassan ya sanar da haka a lokacin rabon kayayyakin tallafin ga wadan da suka gamu da balain gobarar.
Yace garuruwan da suka amfana da kayan agajin sun hada da Yalwa da kuma Giwaran.
Kayayyakin da aka raba sun hada da turmin atamfa da buhunan gero da Dawa da Zannuwan Gado da Yadika.
Da yake karin haske sakataren KH Muhammad Nasiru Ahmed ya ja hankalin wadan da suka amfana da tallafin dasuyi kyakyawa amfani dashi wajan ciyar da iyalinsu.