Barkewar wani kwaro mai suna MALADOMA ta mamaye gonaki a karamar hukumar Guri.
Kwarin yakan kai hari a gonakin Gero da Masara.
Da yake karbar rahoton, Daraktan Janar na Karamar Hukumar, Kwamared Muhammed Gudaji Kazaure ya kafa kwamitin bincike karkashin jagorancin shugaban sashen gona na karamar hukumar Bashir Abdu Kazaure .
Ya bukaci kwamitin da ya fito da mafita tare da ba manoma shawara kan matakan da za a dauka na kashe kwarin a gonakin su
shugaban sashen gona na karamar hukumar Bashir Abdu Kazaure ya ce an tura jami’an su na aikin gona a gonaki daban-daban domin su yi amfani da wani maganin kwari da zai magance yaduwar kwarin
sannan ya yi kira ga manoman da su ba da hadin kai ga ma’aikatan noma da ke halartar filayen noma domin kula da matsalar kwarin.
- Comments
- Facebook Comments