An kama wani da ake zargin dan fashi da makami ne a jihar Kano

0 193

Jami’an tsaron farin kaya, reshen jihar Kano, sun kama wani da ake zargin dan fashi da makami mai suna Abdulrahman Auwal da ke Layin Tankin Magi a karamar hukumar Kura ta jihar.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar, SC Ibrahim Idris Abdullahi, ya tabbatar da kamen a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a jiya Talata.
A cewar sanarwar, jami’an ofishin shiyya na Garun Malam sun cafke wanda ake zargin, yayin da suke lalata taransfoma da igiyar wutar lantarki a kauyen Dakasoye da ke karamar hukumar Garun Malam.
A a cewar sanarwar wanda ake zargin, ya amsa laifinsa kuma za a gurfanar da shi a gaban kotu bayan kammala bincike.

Leave a Reply

%d bloggers like this: