An samu kararraki 34 na cin zarafin mata (GBV) a jihar Yobe

0 66

Rundunar ‘yan sanda a jihar Yobe a jiya ta ce ta samu kararraki 34 na cin zarafin mata (GBV) a jihar daga watan Janairu zuwa yau.
Kakakin rundunar, Dungus Abdulkarim, ya shaida wa manema labarai a Damaturu, cewa kashi 85 cikin 100 na kararrakin na fuskantar shari’a, yayin da rundunar ta samu hukuncin daurin rai da rai a kashi 15 cikin 100 na kararrakin.
Kakakin ya shawarci iyaye da su rika lura da alakar ‘ya’yansu a koda yaushe, tare da lura cewa masu aikata laifin, na iya zama dangi, makwabta ko kuma abokai.
Dungus Abdulkarim ya kuma bukaci masu ruwa da tsaki da su hada karfi da karfe wajen yakar masu cin zarafin yara, wanda zai iya kawo cikas ga ci gaban yara mata da kuma al’umma gaba daya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: