Al’ummar garin Zalanga a jihar Bauchi sun yabawa masu yi wa kasa hidima NYSC

0 92

Al’ummar garin Zalanga dake karamar hukumar Ganjuwa ta jihar Bauchi sun yabawa mahukunta da ‘yan kungiyar masu yi wa kasa hidima (NYSC) bisa gudanar da aikin jinya kyauta a tsakanin al’umma.
A madadin al’ummar yankin a wajen taron wayar da kan jama’a na kwana guda a jiya, hakimin kauyen Zalanga, Yusuf Mohammed, ya nuna jin dadinsa ga shirin da suka kawo musu.
Ya ce taron zai taimaka sosai wajen magance kalubalen kiwon lafiyar jama’a, ya kuma kara da cewa yin hakan zai taimaka matuka wajen taimakawa mutanen kauyukan yankin wajen samun ayyukan kiwon lafiya da ba su samu ba.
Ko’odinetar hukumar NYSC ta jihar Bauchi, Misis Rifkatu Yakubu, ta bayyana cewa an fara gudanar da shirin ne a karkashin shirin na hukumar NYSC.

Leave a Reply

%d bloggers like this: