Wani sabon rahoto da hakumar kididdiga ta kasa NBS hadin guiwa da ofishin yaki da laifuffukan ta’ammali da kwayoyi na majalisar dinkin duniya sun ce .
An fitar da rahotan ne dogaro da bayanan da ofishin majalisar dinkin duniyar ya tattara.
A cewar rahotan wanda aka wallafa jiya an biya kudaden cin hanci a kasa da suka kai kashi 0.35 na maaunin tattalin arzikin kasa na GDP.
A cewar rahotan matsakaicin yawan kudin cin hanci da aka bayar shine naira dubu 8,284 kari akan naira 5,754 da dake zama matsakaici a 2019.
Haka kuma kashi 56 na yan najeriya sun yi hulda da masu rike da mukaman gwamnati a 2023, wanda aka samu ragi daga kashi 63 da ake dashi a 2019.
Sai dai duk da ragin da aka samu, karuwar bazuwar mutanen da suka aikata ayyuka masu alaka da cin hanci da rashawa a kasa da wanda jumillar su yakai mutum miliyan 87 a duk fadin kasa, alkaluman da ke nuna nan samu raguwa kenan idan aka kwatanta da mutane miliyan 117 da aka yi kiyasi a 2019.