An shawarci gwamnatin tarayya da ta cire tallafin wutar lantarki baki daya

0 119

Asusun bayar da lamuni na majalisar dinkin duniya IMF ya shawarci gwamnatin tarayya da ta cire tallafin wutar lantarki baki daya, duk da matsi da tsadar rayuwa da yan najeriya ke fuskanta tun bayan cire tallafin man fetur a watan mayun 2023.

A cewar wani rahoto da Asusun  IMF ya wallafa a shafinsa na yanar gizo, yace gwamnatin tarayya tana tursasa kanta kan abubuwan da suke neman fin karfinta, don haka akwai bukatar ta janye tallafin lantarki kamar yadda ta cire na man fetur.

Cibiyar ta Bretton Woods ta bayar da wannan shawarar a matsayin hanyar da Najeriya za ta bi domin farfado da tattalin arzikin ta da ya shiga wani hali, abin da ke zuwa dai-dai lokacin da gwamnatin tarayya ta ce tallafin wutar lantarki tsakanin watan Janairu zuwa Satumban 2023 ya lakume Naira biliyan 375.8, yayin da masu amfani da wutar lantarki suka biya jimillar naira biliyan 782.6. Asusun na IMF ya yabawa gwamnatin tarayya kan sauye-sauyen da ta aiwatar zuwa yanzu amma ta sake nanata cewa ya kamata a cire tallafin wutar lantarki kamar yadda aka cire a bangaren man fetur.

Leave a Reply

%d bloggers like this: