An tabbatar da mutuwar mutane a wani sabon hari da ’yan bindiga suka kai Jihar Filato

0 158

Jami’an tsaro sun tabbatar da mutuwar mutane a wani sabon hari da ’yan bindiga suka kai a Karamar Jos ta Gabas a Jihar Filato.

A daren ranar Asabar ne ’yan bindiga suka kai harin, inda suka kashe wani magidanci da dansa a yankin Durbi da ke karamar hukumar.

Shaidu sun ce mutanen unguwar sun yi fito-na-fito da maharan, kuma sun yi nasarar kashe daya daga cikin ’yan bindigar.

Wata majiya ta ce mutanen unguwar sun tsare gawar dan bindigar, kafin mataki na gaba da za su dauka.

Amma da yake jawabi kan lamarin, kakakin rundunar tsaro ta ‘Operation Safe Haven’, da ke aikin wanzar da zaman lafiya a Jihar Filato, Kyaftin Oya James, ya ce ’yan bindigar sun yi yunkurin yin garkuwa da mutane ne.

Kyaftin Oya James, ya ce ’yan bindigar sun je ne da nufin yin garkuwa da wani magidanci mai suna Luka Kaze, wanda a garin haka suka kashe dansa.

Kyaftin Oya ya kara da cewa a lokacin da sojoji suka fara kawo dauki ne ’yan bindigar suka harbe dayansu har lahira bisa kuskure. A cewarsa, harbe abokin nasu da sukayi ne ya sa suka harbe Mista Luka Kaze.

Leave a Reply

%d bloggers like this: