Kotu ta bayar da umarnin tsare wani mutum bisa zargin cin zarafin Limamin Masallaci

0 86

Wata Kotun Shari’ar Musulunci da ke zamanta a Kofar Kudu a Jihar Kano, ta bayar da umarnin tsare wani Malam Nasiru Mukhtar, bisa zargin cin zarafin Limamin wani Masallaci da ke Tudun wada.

Ana zargin Mukhtar da shiga Masallacin tare da kai wa Limamin Malam Murtala Sulaiman, hari yayin da yake shirin jan sallar Asuba, a ranar talatar da tagabata.

Rahotanni sun bayyana cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 5 na Asuba, inda Mukhtar ya shiga Masallacin tare shaƙe Limamin.

Kazalika, ya kama shi da damɓe da yayyaga rigarsa, sannan ya lalata na’urar amsa kuwwar limamin, lamarin da ya sa shi kai rahoto ga rundunar ‘yansandan Jihar Kano.

Rundunar ‘yansandan ta shaida cewa tuhumar da ake yi wa Mukhtar, ta yi daidai da sashe na 165 da 166 na kundin laifuka na jihar.

Amma wanda ake tuhumar ya musanta laifin lokacin da lauyan mai shigar da ƙara Aliyu Abidin, ya karanta masa tuhumar a gaban kotu. Daga ƙarshe Alƙalin kotun, Malam Isah Rabi’u Gaya, ya yi watsi da buƙatar neman belin wanda ake ƙara, tare da bayar da umarnin gwajin lafiyar wanda ake zargin a wani asibiti da ke yankin don tantance lafiyar ƙwaƙwalwarsa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: