An yabawa Gwamna Namadi bisa aikin hanyar Kwanar Kuka-Gatsanya-Manaba zuwaTafa

0 212

Shugaban kwamatin ayyuka da sufuri na majalisar dokokin jihar Jigawa Alhaji Yusuf Ahmad Bulangu, ya yabawa Gwamna Malam Umar Namadi bisa aikin hanyar Kwanar Kuka-Gatsanya-Manaba zuwaTafa.

Alhaji Yusuf Ahmad Bulangu ya yi wannan yabo ne lokacin da ya jagoranci Yan kwamatin suka ziyarci wurin aikin, inda ya ce wannan shine aiki na farko da ya fara gabatarwa majalisa bukatar yi.

 Ya bayyana yankin Tafa a matsayin matattarar ruwa da ke haifar da ambaliya ga yankin Hadejia duk shekara, yayin da hanyar ta zamo mahada ga matafiya daga jihohin Arewa maso Gabas.

A nasa jawabin, Alhaji Idi Masta Maji Dadin Jabo ya ce al’ummonin yankin sun kwashe shekaru 15 suna fafutukar neman hanyar Kwanar Kuka-Gatsanya zuwa Tafa dan haka ya godewa Governor Malam Umar Namadi bisa amsa kiran jama’a. Kamar haka kwamatin ya duba aikin gyaran hanyar Auyo zuwa Kafin Hausa akan naira miliyan 989 da aikin sabunta hanyar Yalleman zuwa Kaugama ta wuce Madana mai nisan kilomita 37 akan naira miliyan dubu 8 da 151 da aikin sabuwar hanyar Sule Tankarkar zuwa Maitsamiya ta wuce Gidan Alko mai nisan kilomita 30 akan naira miliyan dubu 7 da 182.

Leave a Reply

%d bloggers like this: