Masana kimiyyar yanayi a Turai sun bayar da wasu kwararan hujjoji da ke tabbatar da cewa har yanzu ba a cimma muhimman manufofin da kasashen duniya suka amince ba na rage dumamar yanayi.
Masanan na Turai sun ce a karon farko ma’aunin yanayin zafi ya zarta digiri 1.5 cikin shekara daya wanda aka kayyade kasa da shekara 10 da suka gabata a babban taron sauyin yanayi na Paris, inda masana suka yi gargadin cewa, idan har dumamar yanayi ya zarta wannan ma’aunin to za a iya fuskantar mummunan sakamako a duniya.
Masanan a hukumar da ke kula da yanayi ta tarayyar Turai sun ce watanni takwas da suka gabata, sun kasance mafi zafi da aka taba gani a tarihi, kuma zafin teku ya ci gaba da karuwa. Farfesa Liz Bentley ita ce shugabar cibiyar nazarin yanayi ta Royal Meteorological Society.