An yi garkuwa da shugaban karamar hukumar Akwanga a jihar Nasarawa

0 153

Wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da shugaban karamar hukumar Akwanga a jihar Nasarawa, Safiyanu Isa Andaha.

Rundunar ‘yan sandan jihar ta ce, an sace shugaban karamar hukumar akan hanyarsa ta yin bulaguro a daren jiya a kauyen Ningo da ke kan titin Andaha zuwa Akwanga, tare da wani dan asalin yankin.

A cewar jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Ramhan Nansel, yace  jami’an tsaro da suka hada da ‘yan sanda da sauran hukumomin tsaro sun fara bin diddigin wadanda suka yi garkuwa da su cikin gaggawa domin ganin an kubutar da mutanen. ‘Yan bindiga dai na ci gaba da gudanar da ayyukansu a yankin Arewa ta tsakiya da kuma Arewa maso yammacin kasar nan duk da cewa jami’an tsaro suna bakin kokarinsu

Leave a Reply

%d bloggers like this: