Hukumar kula da zirga-zirgar jiragen kasa ta Kasa ta kammala tsare-tsaren fara aikin dare

0 132

Hukumar kula da zirga-zirgar jiragen kasa ta Kasa, ta ce ta kammala dukkanin wasu tsare-tsare na fara aiki a cikin dare kafin nan da zango na biyu na shekarar da muke ciki.

Shugaban hukumar ta NRC Fidet Okhiria, ne ya bayyana hakan a lokacin da yake zantawa da kamfanin dillancin labaran Kasa NAN.

A cewar hukumar ta NRC, wannan ya nuna cewa hukumar zata soma zirga-zirgar jiragen kasa daukar kaya shida a rana. Yace hukumar zata kara yawan zirga-zirgar jiragen shida ne a rana a jihohin Lagos zuwa Ibadan, da warri zuwa Itakpe da kuma Abuja zuwa kaduna.

Leave a Reply

%d bloggers like this: