An yi garkuwa da tsohon shugaban jam’iyyar APC

0 242

Wasu ‘yan bindiga sun mamaye tsohon garin Zungeru na jihar Neja inda suka yi garkuwa da tsohon shugaban jam’iyyar APC a karamar hukumar Wushishi, Alhaji Sule Muhammad.

A jiya ne ‘yan bindigar suka kai farmakin inda suka yi ta harbe-harbe kafin su daga bisani suka ranta ana kare.

Wasu mazauna unguwar da suka zanta da manema labarai sun ce an yi garkuwa da tsohon shugaban ne a gidansa da misalin karfe 12 na safiyar jiya yayin da ‘yan bindigar suka raunata ‘yarsa da dansa. Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Neja, DSP Wasiu Abiodun amsa kiran waya da aka yi masa ba, sai dai an tura masa sakon karta kwana amma har zuwa lokacin hada wannan rahoto bai ce komai ba dangane da wannan al’amari.

Leave a Reply

%d bloggers like this: