Gwamnatin Jamhuriyar Nijar ta maka shugabannin kungiyar ECOWAS a kotu

0 212

Gwamnatin Jamhuriyar Nijar karkashin jagorancin Janar Abdourahmane Tchiani ta maka shugabannin kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka ta ECOWAS a kotu kan takunkumin da kungiyar ta kakaba wa kasar bayan kwace mulki da sojoji suka yi.

Shugabannin juyin mulkin sun bukaci kotun ECOWAS da ta gaggauta janye takunkumin da makwabtansu na kasashen yammacin Afirka suka yi musu.

Sakamakon haka, kotun ECOWAS a zamanta a Abuja a ranar Litinin data gabata ta sanya ranar 7 ga watan Disamba, 2023, a matsayin ranar da zata yanke hukunci kan wannan kara. An kakabawa Nijar takunkumin karya tattalin arziki bayan da sojojin da ke kiran kansu Majalisar Tsaro ta Kasa suka hambarar da Shugaba Mohammed Bazoum a ranar 26 ga Yuli, 2023.

Leave a Reply

%d bloggers like this: