An yiwa shugaban ƙasa Muhammadu Buhari allurar rigakafin corona karo na uku

0 197

An yiwa shugaban kasa Muhammadu Buhari allurar rigakafin corona karo na uku, a fadar shugaban kasa dake Abuja.

Hakan na zuwa ne a lokacin da Najeriya ta shiga zagaye na uku na annobar corona bayan an samu karuwar wadanda suke kamuwa da cutar da ninki 5 cikin makonni biyun da suka gabata.

A wani labarin kuma, Uwargidan shugaban kasa Aisha Buhari ta umurci dukkan ma’aikatanta da su tafi hutu har sai an neme su.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun Dr. Mohammed Kamal, babban mataimaki na musamman ga ofishin uwargidan shugaban kasar kan harkokin lafiya.

Kamal ya bayyana cewa ma’aikatan za su cigaba da gudanar da ayyuka ta internet.

Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da ake rade-radin cewa uwargidan shugaban kasar na da juna biyu.

Amma a wata hira da manema labarai, kakakin Aisha Buhari ya musanta jita-jitar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: