An zargi sojojin Mali da aikata kisan gilla kan wasu mazauna kauye akalla 20.

0 337

A ranar 12 ga wanan watan sojojin Mali su ka kama mutanen su 27 a yayin wani samame da suka kai a Diafarabe kusa da Tenenkou na Jihar Mopti.

Tun daga wancen lokacin  danginsu  su ka daina jin duriyarsu.

Wasu mazauna kauyen da lamarin ya auku sun ce wadanda aka kashen ‘yan kasuwa ne da aka kama a wuraren sana’oinsu ,suna me bayyana kisan da na ƙabilanci.

Lokacin da iyalan da wadanda aka hallaka su ka je ganin gawarwakinsu an bukaci da kar su dauki hoto.

Shaidun gani da ido sun fadawa RFI cewar anyi wa mutanen yankar rago sanan aka jefar da gawarwakinsu cikin wasu manyan kaburbura guda uku.

Yankin Diafarabe, wuri ne da mayakan kungiyar Jnim mai alaka da al-Qaida ke kai hare hare kan sojojin Mali da kuma mafarauta ‘yan ƙabilar Dozons.

Leave a Reply