Wani jami’in dan Sanda ya mutum a Libiya jiya juma’a a yayin wani yunkuri na kai farmaki kan offishin Firaminista a Tripolie fadar gwamnatin kasar
Gwamantin hadaka Libiya, ta ce, ta bankado wani shirin cinna wuta a ginin fadar Firaministan da wasu masu zanga zanga suka kudiri anniyar yi.
A kwanaki ukun da suka wuce mumunan fada ya barke tsakanin kungiyoyi masu dauke da makamai a tsakiyar birnin Tripolie lamarin yayin sanadin mutuwar mutun takwas.
Ta cikin wata sanarwa da aka wallafa, gwamnatin hadaƙa da ke da mazauninta a Tripolie ta ce wani sanda ya rasa ransa a harin da wasu da ba’a san ko su waye ba su ka kai wa offishin Firaminsta inda ya ke aikin gadi.
A wasu fayafan bidiyo da kamfanin dillancin labaran Faransa bai tabbatar da sahihancinsu ba anga tarin matasan da aka tarwatsa na nema malaba yayin da ake ta jin karar harbin manyan bindigogi.
Gabanin haka dubban mutane sun gudanar da zanga-zanga cikin lumana a wurare daban daban da ke tsakiyar birnin Tripolie don kira ga Firaministan ƙasar Abdelhamid Dbeibah ya yi murabus.
A jajibirin gudanar da zanga-zangar, Majalisa Dinkin Duniya ta yi kira mahukuntan ƙasar da su mutunta ‘yancin mutane.