Shugaban kasa Bola Tinubu ya jaddada muhimmancin sarakunan gargajiya wajen cigaban kasar nan, inda ya nemi goyon bayansu wajen aiwatar da manufofi da ke shafan rayuwar al’umma kai tsaye.
Ya bayyana hakan ne yayin da ya karbi bakuncin sabon Alaafin na Oyo, Oba Abimbola Abdulhakeem Owoade I, da matarsa Abiwumi da wasu sarakuna daga jihar Oyo a fadar shugaban kasa da ke Abuja.
A cewar sanarwar da mai magana da yawun shugaban kasa, Bayo Onanuga, ya fitar, Tinubu ya taya sabon sarki murna tare da tabbatar da goyon bayansa, ya kuma yabawa ’ya’yan masarautar Oyo da ke aiki a ofishinsa, ciki har da Ambasada Victor Adeleke da ADC Colonel Nurudeen Yusuf, wanda shi ma sarki ne a Ilemonaland.
Alaafin ya tabbatar wa shugaban kasa da cewa sarakunan gargajiya za su ba da cikakken goyon baya wajen tabbatar da cikar burinsa na sauya al’amuran rayuwar al’umma a Nigeria.