An fara gudanar da Atisayen sake tantance wanda sukayi rijistar tallafin jin kai na kasa

0 550

Gwamnatin tarayya ta fara gudanar da atisayen sake tantance wadanda sukayi rijistar tallafin jin kai na kasa, domin inganta shirin rabon tallafin kudi ga ‘yan kasa masu karamin karfi.

Shugabar hukumar kula da rajistar dan kasa, Abisoye Coker-Odusote, ta bayyana cewa akalla gidaje miliyan biyu da dubu dari uku aka riga aka tabbatar da su a matsayin wadanda za su ci gajiyar shirin.

Wannan atisaye na zuwa ne a daidai lokacin da Bankin Duniya ke nuna damuwa kan yadda shirin bai ci gaba ba, kamar yadda aka tsara shi tun bayan kaddamar da shi a shekarar 2023, bayan cire tallafin mai da daidaita kasuwar canji.

A cewar rahoton “Building Momentum for Inclusive Growth” da Bankin Duniya ya fitar, daga cikin gida miliyan goma sha biyar da aka yi niyya, kasa da kashi 40 ne kadai suka samu tallafin har zuwa watan Afrilun da ya gabata, sai dai gwamnatin tarayya ta ce tana aiki kafada da kafada da tawagar hadin gwiwa domin tabbatar da sahihancin bayani da kuma ganin talakawa na hakika ne ke cin gajiyar shirin.

Leave a Reply