A taron rabon kudaden shiga na watan Mayu da aka gudanar a Abuja, gwamnatin tarayya, jihohi da kananan hukumomi sun raba naira tiriliyan 1 da billiyan 681 daga kudaden da aka tara a watan Afrilu da ya gabata, kamar yadda mai magana da yawun hukumar FAAC, Bawa Mokwa, ya bayyana.
Kudaden sun hada da naira biliyan 962 da milliyan 882 na harajin gwamnati kai tsaye, naira biliyan 598. 77 daga harajin VAT, sai naira biliyan 38 da milliyan 862 daga harajin canja kudin lantarki da kuma bambancin canjin kudi na naira biliyan 81 da milliyan 407.
Gwamnatin tarayya ta samu naira biliyan 565 da milliyan 307, jihohi kuma sun samu naira biliyan 556 da milliyan 741, yayin da kananan hukumomi suka samu naira biliyan 406 da milliyan 627, da kuma naira biliyan 152 da milliyan 553 da aka bai wa jihohin da ke da hakkin samun kason kudi na albarkatun kasa. A watan Afrilu da ya gabatan, an samu karin kudaden haraji daga bangarori kamar harajin riba daga man fetur da harajin shigo da kaya, sai dai kudaden harajin kamfanoni sun ragu sosai.