Gwamnatin jihar Sokoto ta sake nanata kudirinta na dakile sayar da giya da sauran kayan maye a fadin jihar,
Gwamnatin jihar Sokoto ta sake nanata kudirinta na dakile sha da sayar da giya da sauran kayan maye a fadin jihar, domin tabbatar da tsaftar zamantakewa da kare al’adun addini.
Gwamna Ahmed Aliyu ne ya bayyana hakan a yayin kaddamar da sabon masallacin Juma’a da aka sake ginawa a garin Shagari, inda ya jaddada cewa gwamnatin sa na goyon bayan ayyukan hukumar Hisbah, wadda ta kwace kuma ta lalata tarin giya kwanan nan.
Gwamnan ya bukaci hukumar Hisbah da ta ci gaba da aikinta ba tare da tauye hakkin dan Adam ba, tare da neman hadin kan jama’a domin ganin an cimma wannan buri cikin nasara.
Haka kuma, ya bayyana cewa gwamnati na ci gaba da sake gina masallatai 63 a fadin jihar, tare da biyan kudin wata ga limamai har ma da masu kula da tsaftar masallatai, yana mai cewa hakan na daga cikin muhimman ayyukan da za su amfani rayuwar jama’a kai tsaye.