Gwamnatin jihar Jigawa ta kafa wani sabon kamfani mai suna Farm Mechanization domin samar da guraben ayyukan yi, karfafa wadatar abinci, tare da taimaka wa manoma samun riba mai yawa a harkokinsu.
Daraktan kamfanin, Dr. Ado Nasiru, ne ya bayyana hakan a cikin wani shirin gidan rediyon Jigawa mai suna Jigawa A Yau, inda ya ce kamfanin zai bude ofisoshi biyu a kowacce mazaba tare da samar da manyan taraktoci guda biyar da kayayyakin aikin gona a kowane yanki.
Ya kara da cewa Gwamna Umar Namadi ya riga ya sayi taraktoci 300 da sauran kayayyakin aikin gona na zamani, da ake sa ran za su iso birnin Dutse mako mai zuwa, domin taimaka wa manoman jihar su koma noman zamani don riba. Dr. Ado Nasiru ya ce gwamnati ta kashe Naira biliyan 27 wajen siyan kayan aikin, inda ya bayyana cewa kamfanin ya kafa wani sashe da zai rika wayar da kan manoma kan dabarun noma na zamani, kuma an tanadi tsauraran matakai na kula domin tabbatar da cewa kayan aikin sun tsaya a jihar kuma manoman Jigawa kadai ne za su ci gajiyarsu.