Gamayyar kungiyar masu bukata ta musamman ta Jigawa ta koka kan karancin masu bukata ta musamman a cikin jerin sunayen kamsiloli
Gamayyar kungiyar masu bukata ta musamman reshen jihar Jigawa ta koka akan karancin masu bukata ta musamman a cikin jerin sunayen kamsiloli masu gafaka da kuma masu bada shawara a karamar hukuma da aka nada a kananan hukumomin jihar nan.
A wata sanarwa da Shugaban kungiyar Honourable Adamu Shu’aibu Jigawar Tsada ya fitar. Ya ce abin takaici ne a duk sunayen sanya suna dokar masu bukata ta musamman ta 2017 ta jihar Jigawa ta amince da baiwa masu bukata ta musamman dama a harkokin siyasa da kuma sanya su a cikin nade naden siyasa dana gwamnati.
Adamu Shu’aibu Jigawar Tsada yana mai cewar wasu kananan hukumomin basa bin umarnin gwamna Umar Namadi wajen bada mukamai ga masu bukata ta musamman din.