Ana cigaba da fargabar cewa za a iya kai hare-haren ta’addanci a Abuja har zuwa 31 ga wannan wata na Disamba

0 107

Wata sanarwar da Hukumar Kula da Shige da Fice ta Kasa ta fitar, ta nuna cewa za a iya kai hare-haren ta’addanci a Abuja babban birnin tarayya, tsakanin ranakun 17 zuwa 31 ga watan Disambar da muke ciki.

A cewar wata sanarwa mai dauke da sa hannun kwamandan hukumar kula da iyakokin kasa, Edirin Okoto, hukumar ta samu rahoto daga fadar shugaban kasa dangane da hare-haren da ‘yan ta’adda na kasashen waje ke shiryawa.

Wadannan ‘yan ta’adda, in ji kwamandan rundunar, sun shirya shigowa Najeriya daga kasar Mali ta Jamhuriyar Nijar.

Ana zargin wani mai suna Drahmane Ould Ali, wanda aka fi sani da Mohammed Ould Sidat, dan kasar Aljeriya ne ke jagorantar harin tare da tallafin wani mai suna Zahid Aminon dan kasar Nijar.

Okoto a cikin sanarwarsa a madadin hukumar ya bayyana cewa, mutanen biyu suna kan hanyarsu ta zuwa Najeriya daga Mali ta hanyar Gao da Jamhuriyar Nijar, cikin wata farar mota kirar Toyota Hilux.

Ya kara da cewa mutane biyun suna tare da wasu ‘yan Najeriya hudu wadanda tuni suka bace a kasarnan.

Leave a Reply

%d bloggers like this: