Gwamnatin jihar Jigawa za ta yi amfani da fasahar zamani domin tabbatar da bin ka’idar hada-hadar filaye

0 68

Gwamnatin jihar Jigawa za ta yi amfani da fasahar zamani domin tabbatar da bin ka’idar hada-hadar filaye da kuma dokokin amfani da filaye a jihar.

Kwamishinan filaye na jiha, Sagir Musa Ahmed ne ya bayyana hakan a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Dutse, inda ya kara da cewa an yi hakan ne da nufin tabbatar da dokar filaye da kuma hana manoma da makiyaya rikici bisa filaye.

Kwamishinan ya bayyana cewa sabuwar dabarar za ta kuma shawo kan matsalar fasa-kwaurin filaye, rabon filaye ba bisa ka’ida ba da kuma sauya manufar amfani da filaye.

Sagir Ahmed ya yi nuni da cewa kula da filaye da rabonsu ba bisa ka’ida ba, sune manyan kalubalen da jihar ke fuskanta.

A cewarsa, an ware dubban kadada na fili ga fannin kiwon lafiya, noma da ilimi domin ayyukan raya kasa daban-daban a fadin jihar.

Sagir Ahmed ya yabawa Gwamna Badaru Abubakar bisa inganta rayuwar al’ummar Jigawa ta hanyar noma, kiwon lafiya, samar da ruwan sha, ilimi da inganta rayuwar mata da matasa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: