Majalisar zartarwa ta tarayya ta amince da kwangiloli 16 da nufin bunkasa karfi da ingancin wutar lantarki a Najeriya

0 80

Majalisar zartaswa ta tarayya, FEC, ta amince da kwangiloli 16 da nufin bunkasa karfi da kuma ingancin rarraba wutar lantarki a fadin kasar nan.

Ministan Wutar Lantarki, Abubakar Aliyu, ya bayyanawa manema labarai na fadar shugaban kasa, bayan wani taro na musamman na FEC da mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya jagoranta a ranar Alhamis a fadar shugaban kasa dake Abuja.

Ya ce babbar matsalar da ke tattare da kamfanin samar da wutar lantarki ta Najeriya, ita ce yadda ake kwashe isasshiyar wutar lantarki da kuma rarraba su.

Ya ce an kuma amince da gina layin da zai kai Kilo Voltave 132 a birnin Ado-Ekiki, jihar Ekiti.

A cewarsa kwangilar zata lakume kimanin dala miliyan 30.8, da kimanin Naira biliyan 8.3.

Ya ce daga cikin ayyuakan akwai gina sabbin tashoshin lantarki na kasa a Oshogbo duka a yankin kudancin kasar nan.

Leave a Reply

%d bloggers like this: